Sabon Sarkin Kuwait Sheikh Nawaf al-Ahmad Al-Sabah ya karbi rantsuwar kama aiki a tau.

Hakan ya zo ne kwana daya bayan sanar da rasuwar Sheikh Sabah.

Sheikh Nawaf - wanda shi ne yariman kasar mai jiran gado a baya - ya sha alwashin yin aiki domin samar da daidaito da tabbatar da tsaro a Kuwait.

Ba a tsammanin Sheikh Nawaf mai shekara 83 zai kawar da kasar daga manufofin cikin gida da na ƙasashen duniya da magabacinsa ya samar - wanda dan uwansa ne.
Sabon sarkin kuwait